Gwamna Ganduje Ya Mikawa Sabbin Sarakunan Kano Da Bichi Takardar Shedar Nadi – AREWA News

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa sabbin Sarakunan Kano da Bichi wasikar shedar nadi a yanzu-yanzu.

Da fari Gwamna Ganduje ya mikawa Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero wasikar shedar nadi ne a matsayin sarki mai daraja ta daya.

Bayan mikawa sarkin na Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ne sai gwamnan ya mikawa na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Da yammacin yau ne dai aka fara bikin bada wasikar shedar nadin ga sabbin sarakunan da gwamnatin Kano ta yi. Inda yanzu haka aka gama baiwa dukkaninsu wasikar shaidar zama sarakuna.

More from this stream

Recomended