Gwamna Buni ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya dakatar da Hon. idrissa Mai Bukar shugaban karamar hukumar Machina makonni 3 bayan da aka rantsar da shi tare da sauran ciyamomin da aka zaba a zaɓen ƙananan hukumomin jihar na ranar 09 ga watan Yuni.

Sakataren yaɗa labaran sakataren gwamnatin jihar, Shu’aibu Abdullahi shi ne ya sanar da dakatarwar cikin wata sanarwa da ya fitar..

Abdullahi ya ce gwamna Buni ya yi amfani da ƙarfin ikon da sashe 2 na dokar ƙananan hukumomi ta shekarar 2019 da aka yiwa gyara ya bashi wajen dakatar  da Bukar saboda nuna rashin ɗa’a da kuma ƙin yin biyayya.

Gwamna Buni ya umarci dakataccen shugaban ƙaramar hukumar da ya miƙa ragama mulki ga mataimakinsa kana ya jiraci umarni na gaba.

More News

An gano gawarwakin ƴan fashin daji 8 a Kaduna

Gawarwaki 8 da ake zargin na ƴan fashin daji ne aka gano bayan da sojoji suka kai farmaki dazukan dake ƙauyen Kurutu dake kusa...

Tinubu ya karɓi Anyim Pius a jam’iyar APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya yi wa  tsohon shugaban majalisar dattawa,Anyim Pius Anyim maraba da zuwa  jam'iyar APC. A makon daya gabata ne Anyim...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...

Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar...