Gwamna Abba Kabir Yusuf Zai Koma APC Ranar Litinin Bayan Ya Bar NNPP

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai koma jam’iyyar APC a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, bayan ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi ta bayyana hakan.

Sanarwar ta ce Yusuf ya taba kasancewa dan APC a shekarar 2014. Ta kara da cewa dalilan mulki, hadin kan kasa da ci gaba ne suka sa ya yanke shawarar komawa jam’iyyar.

Gwamnan ya ce komawarsa APC za ta karfafa hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya tare da inganta ayyukan gwamnati a jihar Kano.

More from this stream

Recomended