Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin jihar, kamar yadda kwamishinan albarkatun ruwa, Ali Makoda ya bayyana.
Makoda ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Laraba.
“Muna kashe naira miliyan 400 a kowane wata wajen sayo man dizal, naira miliyan 387 wajen sayen sinadarai, yayin da kudin wutar lantarki ke daukar naira miliyan 280.
“Akwai kuma wasu kudade. Muna gyara matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar da kewaye. Nan da kwanaki biyu, matsalar za ta kare,” in ji Mista Makoda.
Ya kuma dora laifin karancin ruwa a kan tsofaffin kayan aiki, musamman a cibiyar kula da ruwa ta Tamburawa da ke samar da ruwa ga mafi yawan sassan birnin Kano.