Google zai koma China da aiki

[ad_1]

google

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ma’aikatan kamfanin Google sun soki shirinsa na fara amfani da wata sabuwar manhaja ta matambayi baya bata da za ta rika boye bayanai game da ‘yancin bil adama da addini a China.

A kan wannan ne daruruwan ma’aikatan kamfanin suka rubuta wata wasika ga shugabanninsu inda suke nuna rashin amincewarsu da matakin kamfanin na yin amfani da wannan manhajar da aka dode wa muhimman sassanta.

Sun ce wannan mataki zai sa a rika kallon kamfanin yana mara wa kasar China baya kenan wajen take hakkin ‘yan kasar na samun cikakkun bayanai game da duniyar da suke rayuwa a cikinta.

Kamfanin ya fice daga China shekara takwas da ta gabata ne domin kin amincewa da yayi da dokokin kasar China masu kokarin dakile ‘yancin bil Adama.

Amma wasu rahotanni da suka fito fili na cewa Google yayi nisa wajen kirkirar wata manhajar matambayi baya bata da aka lakaba wa suna Dragonfly.

Kamfani Google ya ki cewa uffan akan batutuwan da ma’aikatansa ke yi kokawa akai.

Amma kafin manhajar ta fara aiki sai hukumomin China sun amince da ita, kuma dole ne manhajar ta dode wasu shafukan intanet da wasu kalamai da bayanai da gwamnatin kasar ba ta amince da su ba.

Wadannan bayanan sun hada da batutuwan ‘yancin dan Adam da na ‘yancin addini.

China ce kasa mafi yawan masu amfani da shafukan intanet a duniya, amma kamfanonin Amurka na fuskantar matsaloli wajen shiga da kayayyakinsu cikin kasar domin tsauraran matakai da kasar ke dauka ta tace dukkan bayanan da ke iya shiga ko ficewa daga kasar.

A misali, shfukan Facebook da Google da Twitter har ma da Instagram ba su da izinin yin aiki a cikin kasar, duk da cewa Google na da ofisoshi haru uku a cikin kasar ta China.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...