Ƴan kasuwa da dama sun yi asarar kayayyaki da dukiyoyinsu na miliyoyin naira a wata gobara da ta kama shaguna 22 a kasuwar Gwarzo, hedikwatar karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano.
Gobarar da ta afku a ranar Litinin, ta jefa mutanen da lamarin ya shafa cikin mummunan yanayi, inda aka ce da yawa daga cikinsu sun yi asarar miliyoyin nairori.
Jami’in yada labarai na shiyyar na karamar hukumar Gwarzo, Rabiu Khalil, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
“Gobarar ta tashi ne da tsakar daren ranar Lahadi kuma an nemi daukin jami’an kashe gobara na jihar. Har sai zuwa safiyar Litinin kafin su iya kashe ta,” in ji sanarwar.