Rahotannin da suke fitowa daga jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya na nuna cewa gobara tlalata dukiyoyi da wasu kayayyaki masu daraja a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke Muna a karamar hukumar Jere a jihar.
An ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Laraba.

Jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), sun kai ziyarar tantance wuraren da lamarin ya faru.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tantance musabbabin tashin gobarar ba.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wata gobara ta ƙone shaguna da dukiyoyi na miliyoyin naira a babbar kasuwar Gamboru da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.