Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar katako da ke yankin tashar jirgin ƙasa a birnin Gombe, inda ta ƙone shaguna da kayayyaki masu yawa, lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa da dama cikin asara mai tsanani.
Lamarin ya faru ne a daren Litinin, bayan rufe kasuwar inda gobarar ta lalata hanyoyin samun abin rayuwa ga mutanen da ke dogaro da kasuwar.
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matuƙar jimami da alhini kan aukuwar gobarar.
A wata sanarwa da Darakta-Janar na harkokin yaɗa labarai na gwamantin jihar, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga al’ummar da abin ya shafa, tare da miƙa saƙon jaje ga ‘yan kasuwa da masu shagunan da suka yi asara.
Sanarwar ta ce gwamnan ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa gwamnatin jihar na tare da su a wannan lokaci mai wahala, inda ya umurci hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da sauran hukumomi masu alaƙa da su da su gaggauta bincike kan musabbabin gobarar tare da kai tallafin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta kafa cibiyar kashe gobara ta zamani domin ƙara ƙarfafa kariyar rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Gobara Ta Lalata Kasuwar Katako A Gombe

