Gobara Ta Laƙume Dukiya Da Gidaje A Gombe

Wata gobara ta tashi a unguwar Sabuwar GRA da ke Jihar Gombe a ranar Laraba, inda ta kona gidaje uku tare da haddasa asarar dukiya da ta kai daruruwan miliyoyin naira.

Mazauna yankin da abin ya shafa sun bayyana damuwarsu, inda suka ce ba su sami damar ceto komai daga gidajensu ba, kuma yanzu suna cikin matsananciyar bukatar tallafi don farfadowa daga wannan ibtila’i.

Malama Sakina, daya daga cikin wadanda gobarar ta shafa, tana kuka ta ce: “Mun rasa komai. Babu wanda ya taimaka mana lokacin da gobarar ta fara. Muna bukatar taimako, musamman daga gwamnati da kungiyoyin agaji, domin mu sake gina rayuwarmu. Kowa ya san yadda rayuwa take da wahala a yanzu.”

Wani mutumi da ya rasa gidansa, Yakubu Baba Gombe, ya soki jinkirin da hukumar kashe gobara ta yi wajen kawo dauki, yana mai cewa: “Kafin su iso, komai ya riga ya kone kurmus.”

Hukuma har yanzu ba ta bayyana musabbabin tashin gobarar ba, yayin da iyalai da dama ke zama babu matsuguni, abinci, ko kayan amfanin gida.

Mazauna yankin sun bukaci gwamnati da ta binciki dalilin gobarar tare da daukar matakan kariya don hana irin haka nan gaba.

More from this stream

Recomended