Gobara ta ƙone fitacciyar kasuwar dake Masaka a ƙaramar hukumar Karu dake jihar Nasarawa.
Wutar gabarar ta fara ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Juma’a kuma kawo yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.
Ƴan kasuwa da dama da abun ya shafa sun bayyana alihininsu kan asarar dumbin dukiyar da suka yi.
Ayuba Ahmad wani ɗan kasuwa ya ce ya kaɗu matuka saboda dukkanin kayansa sun kone kurmus.
“Na dawo daga kasuwa jiya tuni mutane sun biya kudin wasu daga cikin kayan bawai kawai na rasa kuɗina bane a’a yanzu haka ina cikin bashi. Yakamata gwamnati ta kawo mana ɗauki,” a cewar Ayuba a zantawar da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN.
John Uche wani mai sayar da kayan lantarki a kasuwar ya koka kan hargitsi da kuma sace-sace da ya biyo bayan tashin gobarar.