Mutane hudu daga gida daya sun rasa rayukansu a safiyar Laraba, bayan da gobara ta tashi a gidansu da ke Kundila Layin Baba Impossible, a karamar hukumar Tarauni, jihar Kano.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kwashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce jami’insu, Abba Datti, ne ya kai musu rahoto misalin ƙarfe 4:13 na safe.
A cewar Abdullahi, ma’aikatan hukumar sun isa wajen ne suka tarar da bene na ƙasa mai girman kusan kafa 40 da 30, wanda aka yi amfani da shi a matsayin gida, ya riga ya kama da wuta. Gobarar ta cinye dakuna biyu, falo, kicin da banɗaki.
Sanarwar ta bayyana cewa mutane biyar ne suka makale a cikin gidan yayin gobarar. Sun haɗa da mahaifin iyalin, Shodandi mai shekara 43; matarsa Rafi’a mai shekara 30; da ‘ya’yansu mata biyu — Mardiya mai shekara uku, da Yusira mai shekara ɗaya da rabi — waɗanda dukkan su suka mutu.
Sai dai an ce an ceto yaro ɗaya mai shekaru 12, Aminu Shodandi, bayan kokarin jami’an kwashe gobarar.
Hukumar ta mika ta’aziyyar ta ga iyalin da abin ya rutsa da su, tare da jan hankalin jama’a da su yi taka-tsantsan wajen amfani da abubuwan da ka iya haddasa wuta, musamman a lokacin hazo.
Gobara Ta Hallaka Mutane Hudu Ƴan Gida Ɗaya A Kano

