Gobara ta hallaka miji da mata da ‘yarsu a Kano

Kwamishinan 'yan sandan Kano

Hakkin mallakar hoto
Nigerian Police

Rundunar ‘yan sansan jihar Kano a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum uku da suka hada da miji da matarsa da ‘yarsu sakamakon gobarar da ta afku a gidansu da ke Gayawa Tsohowa a karamar hukumar Ungogo.

Tuni dai rundunar ta ce ta kaddamar da bincike kan lamarin.

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jihar Saidu Mohammed ya ce wadanda suka mutun sun hada da yarinya ‘yar shekara biyu.

“Mun samu kiran waya mai daga hankali da safiyar Laraba daga wani mutum Malam Mudassir Abdullahi da misalin karfe 3:57 na safiya, cewa gobara na ci a wani gida.

“Nan da nan sai muka tura ma’aikatanmu da kayan aiki don kashe wutar da misalin karfe na asuba,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya.”

Ya kara da cewa “daga nan sai mutanenmu suka garzaya da wadanda abin ya rutsa da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.”

More from this stream

Recomended