Wata gobara da ta tashi a kasuwar Ita Amodu dake kan tsohon titin Yidi a birnin Ilorin na jihar Kwara ta ƙone kayayyaki da dukiya ta miliyoyin naira.
Gobarar da ta faru ranar Talata ta girgiza mutanen yankin da ƴan kasuwar da suke sayar da katifu, kafet, gam da kuma sauran abubuwa dake da saurin kamawa da wuta.
Da yake magana kan faruwar lamarin mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle ya ce tawagar hukumar sun fuskanci gagarumar gobarar da ta samo asali daga wata mota da aka makare ta da katifa.
“Gobarar ta ƙone babbar motar ta kuma bazu ginin dake kusa dake kunshe da ɗakuna 49 da kuma shaguna 19,” ya ce.
“Duk da ƙarfin gobarar munyi gaggawar ƙokari wajen daƙile wutar daga cigaba da bazuwa. shaguna 12 da kuma ɗakuna 31 aka kare daga wutar.”
Adekunle ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa gobarar da ta samo asali ne daga motar dake maƙare da katifu bayan da katifun suka taba wayar wutar lantarki abun da ya haifar da tartsatsi tare da tashin wuta.