Gobara ta ƙone wani sashe na ginin jami’ar North West

Wata gobara da ta tashi da tsakar ranar Alhamis ta ƙone wani sashe na ginin Gidan Ado Bayero inda jami’ar North West take a ƙofar Nasarawa cikin birnin Kano.

Gobarar ta fara ci ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana a hawa na 9 na ginin inda nan ne sashen karatun Kimiyyar Na’urar Kwamfuta yake.

An ga hayaƙi mai yawa yana fitowa daga ginin abun da ya tilastawa ɗalibai tserewa daga ginin.

Duk da cewa jami’an kai ɗaukin gaggawa da na kashe gobara sun isa wurin da wuri amma an gaza gano musabbabin tashin gobarar.

Ƙokarin jin tabin mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya ci tura.

More from this stream

Recomended