Wata gobara da ta kama da safiyar ranar Litinin ta ƙone wani sashe na gidan gwamnatin jihar Katsina.
Ɓangaren da ya ƙone na jikin ginin ofishin gwamnan jihar inda yake ganawa da manyan baƙi na musamman.
Babu wani dalili da aka bayar kan sanadiyar gobarar ko kuma irin ɓarnar da tayi.
Gobarar ta kama ne a dai-dai lokacin da gwamnan jihar Mallam Dikko Umar Radda ke wata ziyara a ƙaramar hukumar Funtua domin gudanar da taron ganawa da jama’ar shiyar.
Inda za su tattauna kan matsalolin da suke da su da kuma buƙatun da suke so gwamnatin ta mayar da hankali wajen magance su.