Wata gobara da ta tashi da tsakar dare tayi sanadiyar mutuwar wata mata Jummai Sunday mai shekaru 24 da danta Nasiru Rabiu ɗan kimanin shekara 1.
Marigayiyar ta fito ne daga ƙaramar hukumar Eggon dake jihar Nasarawa..
Gobarar ta tashi ne a wani gida dake kasuwar sai da kayan gidaje da kujeru ta Kugbo dake ƙaramar hukumar AMAC ta birnin ta birnin tarayya Abuja.
Shedun gani ido sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne lokacin da matar da ɗan nata suke sharar bacci mai nauyi a ranar Laraba.
Sun ce makota ne da masu jaje suka gano gawarsu a kokarinsu na tattara kayayyakin da suka yi saura bayan da jami’an kashe gobara suka shawo kan wutar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, Lakur Langyi jami’in ɗan sanda dake lura da ofishin ƴan sanda na Karu ya ce sun samu kiran kai ɗaukin gaggawa da tsakar daren ranar Laraba inda suka garzaya wurin suka iske wata mata da ɗanta sun ƙone ƙurmus.
Ya ce ba a san musabbabin faruwar gobarar ba amma tuni suka kaddamar da bincike da gano bakin zaren.