Gobara ta ƙone wani sashe na gidan gwamnatin jihar Katsina

Wata gobara da ta kama da safiyar ranar Litinin ta ƙone wani sashe na gidan gwamnatin jihar Katsina.

Ɓangaren da ya ƙone na jikin ginin ofishin gwamnan jihar inda yake ganawa da manyan baƙi na musamman.

Babu wani dalili da aka bayar kan sanadiyar gobarar ko kuma irin ɓarnar da tayi.

Gobarar ta kama ne a dai-dai lokacin da gwamnan jihar Mallam Dikko Umar Radda ke wata ziyara a ƙaramar hukumar Funtua domin gudanar da  taron ganawa da jama’ar shiyar.

Inda za su tattauna kan matsalolin da suke da su da kuma buƙatun da suke so gwamnatin ta mayar da hankali wajen magance su.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...