
Shagunan da basu gaza uku bane suka ƙone tare da dukiya ta miliyoyin naira a wata gobara da ta tashi ranar Juma’a a Bakin Kasuwa dake ƙaramar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa.
DSC Adamu Shehu mai magana da yawun hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Jigawa shi ne ya sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN haka ranar Asabara a Dutse.
Shehu ya ce gobarar ta ƙone shaguna uku da wata rumfa sai kuma wani sashe na wani masallaci.
Ya ce misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Juma’a jami’an ofishin hukumar dake Hadejia suka samu kiran kai ɗaukin gaggawa kan gobara da ta tashi rukunin shagunan Na Malam Zangi dake Bakin Kasuwa.
Ya kara da cewa kafin su isa gurin tuni gobarar ta cinye shaguna uku da wata rumfa amma sun samu nasarar shawo kan gobarar da taimakon jami’an hukumar kashe gobara.