Giwa ta hallaka sojan Birtaniya a Malawi

Mathew Talbot

Hakkin mallakar hoto
MOD

Wata giwa ta hallaka wani soja dan Birtaniya a yayin da yake wani aiki na dakile masu farauta ba bisa ka’ida ba a kasar Malawi.

Mathew Talbot mai shekara 22 na tawagar 1st Battalion Coldstream Guards, na aiki ne a gandun dajin Liwonde National Park a ranar biyar ga watan Mayu lokacin da dabbar ta kai masa hari.

Shugabansa, Laftanal Kanal Ed Launders ya ce soja Talbot mutum ne mai ”kwazo da kuma son mutane.”

Sakatariyar Tsaro Penny Mordaunt ta ce ya kware sosai a aikin nasa sannan yana da matukar karfin hali.”

Ta kara da ce wa: ”Wannan mummunan lamarin da ya faru tuni ne na hadduran da rundunar sojinmu ke fuskanta a kullum, a yayin da su ke kokarin kare daya daga cikin dabbobin da su ka fi barazanar bacewa a doron kasa daga mutanen da ke son su karar da su domin biyan bukatun kansu.”

Fadar Kensington ta ce Yariman Cambridge yana rubuta wata wasika zuwa ga ‘yan uwan soja Talbot domin yi musu ta’aziya.

Soja Talbot mutumin yankin West Midlands ne kuma yana kan aikinsa na farko da aka tura shi inda da lamarin ya faru, a cewar ministan tsaro.

Hakkin mallakar hoto
MOD

Image caption

Mathew Talbot ya amince zai taimakawa ayyukan yaki da farauta ba bisa ka’ida ba

Tawagar sojojin Birtaniya da kuma kungiyar da ke tsare dazuka African Park Rangers, suna tafiya ne cikin ciyawa wacce ta kai tsawon mita 2.1 – a lokacin da suka tarar da wasu giwaye da ba su gani da farko ba.

Daya daga cikin su sai ta kai wa soja Talbot hari. Jim kadan sai ya mutu saboda raunukan da ya samu. Shi kadai ne daga cikin tawagar ya yi fama da raunuka.

Ya mutu ya bar mahaifinsa Steven, da mahaifiyarsa Michelle, da ‘yan uwansa mata Aimee da Isabel da kuma budurwarsa Olivia da kewa.

A cikin wata sanarwa, ministan tsaron ya ce soja Talbot bai saba da Afirka ba, kuma ya amince da taimakon kungiyar dakile farauta ba bisa ka’ida ba a Malawi.

”Yana da tsabar son sanin tarihin rundunar soji, saboda haka ya yi farin ciki sosai da kasancewa cikin tawagar wacce aka sani da tarihi mai tsawo da kuma kyau,” a cewarsa.

Hakkin mallakar hoto
MOD

”Operation Corded” shi ne lakabin da aka yi wa tawagar ta yaki da farauta ba bisa ka’ida ba a Malawi, wacce ke taimakawa wajen koyar da masu lura da gandun daji a cikin wani yunkuri na dakile masu farautar namun daji ba bisa ka’ida ba.

Ana koya wa masu lura da gandun dajin abubuwa da dama kamar, kama mutane da kai sumame da kuma sadarwa – tare da tawaga ta farko da aka aika a Agustan 2017.

Tsohon sakataran harkokin tsaro Gavin Williamson, ya bayyana cewa za a fadada tawagar yaki da farauta ba bisa ka’ida ba ta Birtaniya wacce za ta koyar da masu kula da gandun daji a Malawi – tawagar ta sojojin dai ta ninka masu kula da gandun daji da ke karkashin koyarwar sojoji har zuwa 120 a shekara ta 2018.

Babban kwamandan tawagar da Talbot yake, Majo Richard Wright ya ce duk da bai dade da sanin Talbot ba, “kullum dai yana sa ni dariya.”

Laftanal Kanal Launders ya kara da cewa: ”Yan uwan Matthew na tawagar Coldstream Guards sun so shi sosai. Za mu yi mutukar kewar kwazonsa, da kuma yadda ya ke son sa mutane dariya.”

Farautar giwaye babbar matsala ce a duk fadin Afirka – wasu suna kiyasta cewa ana kashe 30,000 a kowace shekara kuma a yanzu a kalla 450,000 ne kawai suka rage.

A wurare da dama tamkar ana yaki ne da masu farautar – shi yasa dakarun Birtaniya ke koyar da masu kula da gandun dajin.

Amma mutane da dama suna da ra’ayoyi daban-daban kan yadda za a dakile cinikin hauren giwa ba ta halaliyar hanya ba.

Kiraye-kiraye a fadin duniya – wanda ke da goyon bayan kasashe kamar su Kenya – suna son a dakile cinikin hauren giwa domin a hana masu aikata laifuka biyan bukatunsu.

Amma wasu kasashen kudancin Afirka wadanda ke da yawancin giwayen Afirka sun yarda da cewa cinikin hauren giwa ta halaliyar hanya zai inya janyo kudaden da za a iya amfani da su wajen kare shuke-shuke da kuma dabbobi.

More from this stream

Recomended