Ginin bene mai hawa uku ya ruguzo a Lagos

Wani ginin bene mai hawa uku dake kan layina Adeniyi a Lagos Island ya ruguzo.

Akalla mutane uku mazauna gidan aka samu damar cetowa aka kuma garzaya da su asibiti jim kadan bayan ruguzowar ginin a ranar Alhamis.

Gbenga Omotoso,  kwamishinan yada labarai na jihar shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wani sako da ya wallafa a Facebook inda ya ce ba a tabbatar da musabbabin rushewar ginin ba.

“Ginin bene mai hawa uku ya ruguzo a Lagos Island, ” a cewar sakon da ya wallafa.

Ya kara da cewa jami’an aikin ceto na cigaba da bincike baraguzan ginin ko za su gano karin wasu mutanen da abun ya shafa.

More from this stream

Recomended