Gidan wata ministar Tinubu a Abuja ya kama da wuta

Gidan karamar ministar babban birnin tarayya (FCT), Dr Mariya Mahmoud, ya kama da wuta a yau Lahadi.

Rahotanni sun ta tattaro cewa wutar ta fara ne a gidan da ke unguwar highbrow da ke Asokoro a Abuja da rana.

Rahotannin sun ce jami’an kashe gobara sun kasa kai dauki da wuri, lamarin da ya kara ta’azzara wutar.

Duk ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba, mai taimaka wa ministar kan harkokin yada labarai Mista Austine Elemue ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba.

Ya ce ana kan binciken musabbabin barkewar gobarar.

More from this stream

Recomended