Gianluigi Buffon ya amince da sake komawa Juventus

Gianluigi Buffon

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Gianluigi Buffon ya taka leda sau 24 a Paris St-Germain

Tsohon golan Italiya Gianluigi Buffon ya amince ya sake koma Juventus bayan shafe kaka daya kacal a Paris St-Germain.

Buffon, mai shekara 41, ya shafe shekara 17 a Turin kafin ya koma Paris St-Germain a kakar da ta gabata.

A watan da ya gabata ne ya sanar da cewa zai bar PSG, kuma BBC ta fahimci cewa za a gwada lafiyarsa a Juventus ranar Alhamis.

Golan, wanda ya buga wa Italiya wasa sau 176, yana daga cikin ‘yan wasan da suka fi samun nasara a fagen tamaula.

Ba ya ga gasar cin kofin duniya da ya lashe a 2006, Buffon ya lashe gasar Serie A sau tara da Coppa Italia hudu. Ya kuma lashe gasar Lig ta Faransa a kakar da ta gabata.

Buffon zai zamo dan wasa na uku da Juventus ta dauka kyauta a bana bayan da ta dauki Aaron Ramsey daga Arsenal da kuma Adrien Rabiot daga PSG.

More from this stream

Recomended