Gbajabiamila Ya Bukaci Goyon Bayan Arewa Don Tabbatar Da Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu

Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya bukaci shugabannin siyasa na Arewacin Najeriya da su mara wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya domin samun nasarar sake tsayawa takara a zaben 2027.

Gbajabiamila ya yi wannan kira ne a wani taron tattaunawa na shekarar 2025 da kungiyar tsofaffin ‘yan majalisa daga Arewacin Najeriya ta shirya a birnin Abuja.

A cewarsa, yankin Arewa na cin moriyar gwamnati mai ci a fannoni da dama, kuma hakan na nuni da cewa shugaba Tinubu ba shugaban Kudu kadai ba ne, sai dai shugaban kasa na kowa da kowa a fadin kasar.

A kalamansa: “Shugaban kasa Tinubu ba shugaban Kudu kawai ba ne; shugaban kasa ne na kasa baki daya, wanda ya hada kowane yanki cikin tafiyar mulkinsa.

“Daga muhimman ayyukan raya kasa zuwa gyaran manufofi, Arewa na amfana da gwamnati mai gaskiya da ke neman adalci da zamanin walwala ta bai daya.

“Muna shimfida tubalin ginin makoma mai inganci tun daga yanzu, kuma abu ne na adalci a bar shugaban ya kammala abin da ya fara.”

Gbajabiamila ya jaddada cewa irin ci gaban da yankin Arewa ke samu a karkashin gwamnatin Tinubu ya kamata ya zama dalilin da zai karfafa musu guiwar goyon bayan sake zabensa a 2027.

More from this stream

Recomended