
Majalisar dattawa ta gayyaci babban sifetan ƴansanda na kasa, Muhammad Adamu kan ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma barayi masu ɗauke da makamai dake cigaba da cin karensu a sassa daban-daban na kasarnan.
Ana sa ran babban sifetan zai bayyana gaban majalisar a mako mai zuwa.
Majalisar ta tsayar da matakin gayyatar babban sifetan ne biyo bayan wani kudiri da sanata, Shehu Sani ya gabatar a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Sani ya gabatar da kudirin ne biyo bayan kisan wata ma’aikaciyar agaji yar kasar Birtaniya, Faye Mooney da abokin aikinta, Matthew Oguche a wani gidan shakatawa dake Kajuru a jihar Kaduna.
Dukkansu sun mutu yayin musayar wuta tsakanin masu garkuwa da mutane da kuma yansandan kwantar da tarzoma dake gadin wajen.