Gabashin Kogin Bahar-Rum: ya sa rikici tsakanin Girka da Turkiyya ya ƙi ƙarewa

  • Jonathan Marcus
  • Wakilin BBC kan Tsaro da Diflomasiyya, Lithuania

Cikin makonnin da suka gabata, an rika samun ƙaruwar tashin hankali a gabashin tekun Bahar Rum, lamarin da wasu ke ganin daɗɗaden rikici tsakanin Turkiyya da Girka kan albarkatun mai.

Turkiyya ta fito gadan-gadan tana neman albarkatun mai musamman iskar gas, inda ta tura jiragen yaƙinta na ruwa su raka jirgin binciken. An kuma kara tsakanin sojojin nata da na Girka har ta kai ga Faransa ta shiga rikicin tana marawa Girkawa.

A baya-bayan nan kuma an sanar da cewa wasu jiragen yaƙi samfurin F-16 daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun fara isa wani sansanin soji da ke Crete domin yin atasaye da takwarorinsu na Girka. Sai dai sun ce wannan abbu ne da suka saba yi.

Shin me ke faruwa ne? Ko wannan rikicin na da tasiri da albarkatun man da ke jibge a ƙarkashin teku? Me yasa kaashen da ke nesa da yankin ke shiga cikin maganar da bai kamata a ce ta shafe su ba? Kuma mene ne dalilin da yankin gabashin Bahar Rum ke ƙara faɗawa cikin rikicin siyasa?

Abin da ke faruwa ma da matuƙar hatsari, yana da sarƙaƙiya kuma dangantakar ƙasashen yankin za ta ƙara taɓarɓarewa.

Ƙarfin fada-a-ji na Turkiyya na ƙaruwa

Duk da cewa binciken iskar gas ce ummul aba’isin rikicin, amma asalin matsalar ta taso ne daga daɗaɗɗiyar matsalar da ke tsakanin Girka da Turkiyya.

Matsalar kuma babba ce, ga shi kuma sai kara bunkaa ta ke yi. Wata fargabar da ake yi ita ce idan ƙasashe suka ci gaba da dunkulewa kan adawa da Turkiyya, wannan na iya sa zuciyar Turkiyyar ta kara bushewa.

Batun ya kuma nuna yadda ƙarfin faɗa ajin Amurka ke ƙara raguwa a yankin.

Shugaba Donald Trump ya dakatar da sayar wa Turkiyya jiragen yaƙi samfurin F-35 bayan da ta sayo wasu rokokin Rasha masu iya kakkaɓo rokoki. Amma Amurka ba ta mayar da hankalinta wajen matsa wa Turkiyya kan matsalolin tsaro da take jawo ma ta a wurare kamar na Syria da na cikin ƙungiyar tsaro ta Nato ba.

A kan haka ne Jamus ta shiga tsakani domin sasanta Girka da Turkiyya, amma sai Faransa ta fito tana goyon bayan Girka.

Bari mu duba matsalolin ɗaya bayan ɗaya:

Makamashi

A wani mataki, matsalar gaba dayanta na da alaƙa da iskar gas ne. Ƙasashen yankin masu yawa sun gano tarin iskar gas ko kuma suna bincikensa. Wannan na iya haifar da batutuwa daban-daban. A gefe guda batun na iya iza wutar kishin ƙasa, kuma zai ta’azzara rikicin kan iyakokin ƙasashen musamman na cikin teku.

Duka yarjenoyoyin da aka so kullawa kan iyakokin sun tayar da hankula. A bara Turkiyya ta kulla wata yarjejeniya da gwamnatin Libya kuma daga nan ta ci gaba da binciken iskar gas a yankin da Girka ta ke kallo a matsayin wurin da take da ikon gudanar da ayyukan kasuwancinta.

Bayanan hoto,
Wata na’urar hako mai a cikin kogin Bosphorus da ke kan hanyar zuwa tekun Bahar Rum domin ayyukan bincike

Al’amura sun dagule. A farkon wannan watan Girka da Masar sun kulla wata yarjejeniya da ta shata kan iyakokinsu na teku, matakin da ya sa Turkiyya ta ƙara kaimin binciken iskar ta gas da tura jiragenta na ruwa ɗauke da sojojinta na yaki can.

Amma abin lura shi ne duk da cewa ayyukan haƙo mai da iskar gas na iya tayar da hankali, dole a samar da tsarin da zai bayar da damar cin gajiyar albarkatun man kafin kowa ya iya amfana.

Tilas a samar da bututun da zai riƙa fitar da man ko gas ɗin daga yankin zuwa kasuwa. Bututun zai ratsa yankunan teku na ƙasashen idan har suna son amfana da albarkatun musamman daga kasuwannin da ke Turai.

Cyprus

Wannan ƙasar ta kasance cibiyar rigimar da ke tsakanin Girka da Turkiyya tun bayan da dakarun Turkiyyar suka mamaye tsibirin bayan da Girka ta mara wa juyin mulkin da aka yi a can a 1974, kuma ta ayyana ƙasa mai zaman kanta a arewacin Cyprus. Wannan na cikin batutuwan da suka gina ƙiyayyar da ke tsakanin Girkawa da Turkawa da ta fara tun gabanin kafa ƙasar Turkiyya ta yanzu.

Kuma duk da yunƙurin diflomasiyya da aka sha yi – wanda aka sa ran shigar da Turkiyya cikin Tarayyar Turai zai sa a warware matsalar ta Cyprus – matsalar sai ƙara tsawo ta ke yi.

A halin yanzu babu alamar Turkiyya za ta shiga Tarayyar ta Turai. Wannan na cikin dalilan da suka kara dagula dangantakarta da kasashen Turai.

‘Sababbin jagororin Daular Ottoman’

Cikin manyan matsalolin da suka sa Turkiyya daukar tsauraran matakan kan dangantakarta da kasashen waje, akwai wanda wasu ke kallo a matsayin yunƙurin farfado da tsohuwar daular Usmaniyya.

Turkiyya ta sauya alkiblarta tun baya Yaƙin Cacar Baki da kasar ta riƙa bin tafarkin rarrabe batutuwan addini da na mulki. Yanzu ta fi karkata zuwa bin tafarkin addinin Islama a harkokinta na siyasa.

Bayanan hoto,
Wani jirgin binciken mai tare da jiragen yakin Turkiyya na ruwa da ke masa rakiya cikin wannan watan

Turkiyya na kuma ji cewa ƙawayenta sun ki mara wa muradunta na ƙasa baya – musamman a kan yaƙin Syria – inda ta ce kungiyar Nato da Amurka sun kyale ta tana shan wahala.

Saboda wannan ne ta nemi mafitar da a ganinta za ta biya ma ta buƙatunta, wanda yasa ta fara ƙulla ƙawance da Rasha da Iran. Nasarorin da ta samu sun bata damar kulla yarjejeniya da gwamnatin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke mara wa baya a Libya.

Yayin da Turkiyya ke goyon bayan hwamnatin da ke Trabulus, kan yakin basasar da ke faruwa, Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuwa na goyon bayan ɓangaren Janar Khalifa Haftar ne da ke iko da habashin Libya.

Wannan yaƙin ya kasance na nuna ƙarfin ikon kasashen yankin ne wanda ya ƙara wa Turkiyya ƙarfin faɗa a ji har ta kai ga ita ce babban dalilin da gwamnatin ta Libya ke bisa mulki kawo yanzu.

Rikicin Libya ya zurfafa kiyayyar da ke tsakaninta da Masar. Kuma dangantakarsu ta diflomasiyya ta kara yin tsami bayan da aka hamɓarar da gwamnatin Ƴan uwa Musulmi ta Muhammad Morsi a Masar wanda Turkawa ke kallo a matsayin abokiyar tafiya.

Bayanan hoto,
Turkiyya na adawa da dakarun Janar Haftar a Libya, dakarun da Masar ke mara wa baya

Saboda haka ana iya cewa rikicin da ke ruruwa a yankin gabashin tekun Bahar Rum binciken albarkatun mai da gas ya haifar da shi, amma akwai sauran labari da sai an duba tarihi.

Akwai kuma tsofaffin matsaloli da dangantakar diflomasiyya da ke tasowa da ka iya jawo bababn rikici ya ɓarke.

Kuma idan akwai wani yanki da a halin yanzu ke buƙatar a shiga tsakanin ƙasashen da ke cikinsa, to wannan yankin shi ne na gabashin Bahar Rum. Amma wane ne ya dace ya shiga tsakani? Kuma anya ƙasashen yankin na son a sasanta su kuwa?

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...