
Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya ta ce jami’anta sun fara farautar wasu fursunoni 7 da suka tsere daga gidan gyaran hali dake Ilesa a jihar Osun da tsakar daren Talata.
Abubakar Umar mai magana da yawun hukumar ya ce fursunonin sun tsere ne da misalin karfe 02:00 na dare bayan da ruwan sama ya ruguzo da katangar da ta kewaye gidan gyaran halin.
Umar ya ce shugaban hukumar, Sylvester Nwakuche ya bayar da umarnin gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.
Mai magana da yawun hukumar ya ce hukumar na hada kai da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma domin sake kama fursunonin da suka tsere.
Ya kara da cewa ana cigaba da aiki tukuru domin kara tsaurara matakan tsaro a gidan gyaran halin.
Umar ya roki jama’ar gari da su bayar da gamsassun bayanai da za su taimaka wajen sake kama mutanen.