Fursunoni 3,413 Ne Suke Jiran A zartar Musu Da Hukuncin Kisa A Nigeria

Hukumar Kula Da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya ta sanar da cewa fursunoni 3,413 ne ke zaman jiran a zartar musu da hukuncin kisa kuma suke tsare a gidajen gyaran hali daban daban a kasarnan.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Umar Abubakar shi ne ya sanar da haka cikin wata tattaunawa da yayi da kafafen yada labarai a Abuja.

Ya ce jumullar daurarun da suke jiran zartar musu da hukuncin kisa sun hada da maza 3,341 da kuma mata 72.

Ya kuma kara da cewa ya zuwa ranar Litinin 18 ga watan Disamba akwai jumullar dauraru 77,849 da suka hada da maza 76,081 sai kuma mata 1,768 a gidajen gyaran hali dake kasarnan.

Mai magana da yawun hukumar ya ce kaso 69 cikin 100 na wadanda suke gidajen gyaran na zaman jiran a yanke musu hukunci ne ma’ana suna zaman sauraron shari’a.

More from this stream

Recomended