Fursuna Mafi Tsufa A Nijeriya Ya Cika Shekaru Ɗari Cif A Duniya

[ad_1]








Me yafi daɗi ga mutumin da shekarunsa suka ‘ketare saba’in sama da ya samu kanshi a cikin iyalanshi cikin ‘koshin lafiya da kwanciyar hankali? Lokaci ne da mutun ke bu’katar hutu tare da nutsuwa gurin kusanci ga Ubangiji. Lamarin ba haka ya zo ba ga wani tsoho mai suna Pa Celestine Egboluche da yayi bikinsa na cika ɗan shekara ɗari da haihuwa a gidan kaso.

Shekarar da ta gabata ne majiyarmu ta sami labarin tsohon ɗan shekara 99 da ke gar’kame tare da ɗansa mai suna Paul da kuma wani ɗan uwansa ɗan shekara 78 mai suna Kanayo Arinze a gidan kaso sakamakon wani rikici da suka yi a kan wani fili wanda yayi sanadiyyar mutuwar wani mutum.

Lokacin da aka yi rikicin tsoho Celestine yana ɗan shekaru 83, a yanzu kuma ya cika shekaru ɗari cif wanda hakan ya sa ya zamo fursuna mafi tsufa a Nijeriya. An yanke wa tsohon wanda ya shafe shekaru 17 a gidan kaso hukuncin kisa sakamakon laifin da aka ce ya aikata.

Abin takaici ne a ce a lokacin da wasu tsofaffin da suka yi dacen cimma irin shekarunsa suke hannun ‘ya’ya da jikoki cikin so da kulawa, amma shi Celestine yana can gar’kame a layin masu sauraron ranar da za a ‘kaddamar da hukuncin kisa a kansu. In ma ba a kaddamar da kisan ba, zai iya karasa rayuwarsa a can kamar yadda ya shafe shekaru 17 yana saurare.

A yanzu haka an sami wata ‘kungiya mai zaman kanta, ‘Global Society for Anti-corruption’, da ke fafutuka kan a taimaka a sake shi.

An ce tsohon ya shafe shekaru 17 ɗin yana fama da ciwon suga. K’ungiyar ta ro’ki Gwamnatin Tarayya da gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, kan su yafe masa, tare da ɗansa da kuma ɗan uwansa mai shekaru 78.




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...