
Shugaban jam’iyar APC na kasa,Nentawe Yilwatda ya ce Siminalayi Fubara gwamnan jihar Rivers shi ne jagoran jam’iyar APC a jihar.
Yilwatda ya bayyana haka ne lokacin da ake zantawa da shi a cikin shirin Hard Copy na gidan talabijin din Channels.
Ya ce jam’iyar APC ta bawa gwamnoni dama su jagoranci jam’iyar a matakin jiha tare da shawartar su da su jawo kowa a jiki tare da kaucewa watsi da wani tsagi na yan jam’iyar.
“Kasancewarka shugaba baya na nufin zaka tauye hakin rukunin wasu mutanen da suke karkashinka saboda haka muke bada damar jawo kowa a dama da shi,
Yilwatda ya kara da cewa rawar da yake takawa a matsayin shugaban jam’iyar shi ne tsara yadda abubuwa za su gudana a matakin jiha a maimakon zaba musu shugabanni.
Da aka tambaye shi ko Siminalayi Fubara shi ne jagoran APC a jihar ya amsa da cewa tabbas shi ne jagoran APC a jihar.

