Firaministan kasar Indiya, Narendra Modi yayi alƙawarin bayar da tallafin tan 20 na kayan jinkai ga al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa a Najeriya.
Modi ya yi alkawarin ne a ranar Lahadi, bayan da aka bashi lambar girma ta GCON wacce ita ce ta biyu mafi girma a Najeriya.
Ƴan Najeriya da dama ne dai ambaliyar ruwa ta raba da muhallinsu a wannan shekara. A cikin watan Satumba magidanta da dama dake Maiduguri babban birnin jihar Borno ambaliyar ruwa ta raba da gidajensu bayan da madatsar ruwa ta Alau ta fashe.
Firaministan ya ce tallafin nasa wani ɓangare ne na taimakawa ƙoƙarin da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ta ke yi kan magance halin ƙunci da ambaliyar ta jefa mutane a ciki.
Ziyarar ta Modi ita ce irinta ta farko da wani firaministan kasar Indiya ya kawo Najeriya a kusan shekaru 20 tun bayan da tsohon Firaministan Manmohan Singh ya kawo a shekarar 2007.
Firaministan na ƙoƙarin ƙara ƙarfafa alaka a tsakanin ƙasashen biyu.