Fasto na neman a taimaka masa ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga

Micah Sulaiman limamin majami’ar St. Raymond Catholic Church dake Damsa a Gusau jihar Zamfara ya roƙi a taimake shi domin ya samu ƴanci.

A wani fefan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 51 da ya yaɗu a soshiyal midiya Sulaiman dake sanye da  wata shuɗiyar riga da gajeren wando an nuno shi zaune a ƙasa inda yake kiran a taimaka masa.

Wasu ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da Sulaiman ranar 22 ga watan Yuni daga gidansa dake cikin harabar cocin a Gusau babban birnin jihar.

Faston ya ce shi kaɗai ne ƴan bindigar suke tsare da shi..

“Ina roƙon a taimaka mini na fita daga wannan wurin. Ƴan fashin dajin nan sun faɗa mini cewa basa ajiye mutane su daɗe anan.Mutane ba sai kaiwa mako ɗaya anan,”ya ce.

“Sun faɗa mini cewa kashe mutum ba abu ne mai wuya ba a wurinsu.”

More from this stream

Recomended