
Wani jirgin saman kamfanin Air Peace a ranar Lahadi ya kauce ya yi cikin dajiĀ daga kan titin sauka da tashin jiragen sama a lokacin da jirgin ya ke sauka a filin jiragen sama na birnin Fatakwal.
Kamfanin Air Peace ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Osifo-Whiskey Efe mai magana da yawun kamfanin ya fitar.
A cewar sanarwar lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.
Sanarwa ta ce jirgin mai mai nambar tashin jiragen sama ta P47190 mallakin kamfanin da ya taso daga Lagos zuwa Fatakwal kuma ya kauce daga titin jirgi bayan da ya sauka kalau.
“Jirgin ya kauce kadan daga kan titin jirgin ba tare da ya samu wani lahani ba,”
A cewar Air Peace dukkanin fasinjojin sun sauka lafiya lau cikin nutsuwa ba tare da wani ya ji ciwo ba.