
Hukumar FAAN dake lura da filayen jiragen sama na Najeriya ta ce wani jirgin sama mallakin kamfanin jiragen Enugu Air ya samu matsala da giyar saukarsa ta tayar gaba lokacin da yake sauka a filin jirgin saman Akanu Ibiam dake jihar Enugu bayan da ya ta so daga jihar Lagos.
FAAN a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Henry Agbebire daraktan hulÉ—a da jama’a na hukumar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 07:10 na daren ranar Alhamis a lokacin da jirgin ke sauka titin jirgin sama mai lamba 8 dake filin jirgin
Hukumar ta ce jirgin mai nambar rijista SN-BZN ya kafe cak yaki motsi a titin jirgin jim kaÉ—an bayan saukarsa.
Agbebire ya tabbatarwa jaridar The Cable cewa jirgin da ya mallakin kamfanin Enugu Air.
Sanarwa ta ce jami’an agajin gaggawa sun garzaya ya zuwa wurin domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da kuma kare filin jirgin.
“Dukkanin fasinjoji da ma’aikatan jirgin an sauke su tare da kwashe su lafiya a cikin motoci ya zuwa ginin filin jirgin saman. An kammala aikin kwasar ta su lafiya ba tare da rauni ba da karfe 07:48,” a cewar sanarwar.

