
An samu nasarar gano mutum daya da ya tsira da ransa a cikin fasinjojin jirgin saman kamfanin Air India da ya yi hatsari.
Jirgin na Air India ya fadi ya kama da wuta jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Ahmedabad a ranar Talata.
Fasinjoji 242 ne a cikin jirgin dake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Gatwick dake birnin London.
Kafar yada labarai ta BBC rawaito kwamishinan yan sandan birnin Ahmadabad, GS Malik na cewa akwai mutum guda da ya tsira da ransa wanda yake zaune a kujera mai namba 11A a cikin jirgin kirar Boeing 787-8 Dreamliner.
“Yana can asibiti yana samun kulawar, “ya ce.
Sunayen fasinjojin da hukumomin suka fitar ya nuna cewa Vishwash Kumar Ramesh dan kasar Birtaniya shi ne fasinja dake zaune a kujera mai namba 11A.
An rawaito Ramesh na cewa ” Dakika 30 bayan tashin jirgin an ji wata kara mai karfi sai kuma jirgin ya fadi lamarin ya faru da gaggawa,”