Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru biyar da kotu ta yanke masa kan zargin aikata cin hanci da rashawa.

Lawan wanda ya kasance  shugaban kwamitin wucin gadi na  majalisar wakilai ta tarayya da aka naɗa domin ya binciki badaƙalar kuɗin tallafin man fetur a shekarar 2012 an yanke masa ɗaurin zaman gidan yari bayan da ya karbi  toshiyar baki ta $500,000 daga fitaccen ɗan kasuwan nan Femi Otedola domin ya wanke kamfaninsa na Zenith Oil daga dukkanin zarge-zargen da ake wa kamfanin.

An kuma tura shi gidan yari a shekarar 2021 bayan da aka same shi laifin neman a bashi toshiyar baki har dalar Amurka miliyan $3 daga hannun Otedola.

Fefan bidiyon da Otedola ya saki a matsayin sheda ya nuna  yadda Lawan yake cusa kuɗin da aka bashi  a cikin babbar rigarsa da kuma ƙasan hula.

Bayan sakin nasa Lawan ya miƙa godiyarsa ga Allah da yan uwa da kuma abokan arziki bisa yadda suka kasance da shi a cikin halin da ya samu kansa.

Ya ce a yanzu ya bude wani sabon shafi na rayuwarsa bayan fitowarsa daga gidan yarin.

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...

An kashe shugaban wata makaranta a Abuja a cikin gidansa

Wasu mutane da kawo yanzu ba a san ko su waye ba sun kashe, Bala Tsoho Musa shugaban makarantar Abuja Rehabilitation Centre. Musa wanda aka...