
Hakkin mallakar hoto
Reuters
Kungiyar OPEC da sauran kasashe masu samar da mai suna son ganin sun ci gaba da cin moriyar tashin farashin mai a duniya
Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, OPEC, da kawayenta suna shirin kara tsawon lokacin rage yawan man da suke samarwa, domin ganin farashin danyen man ya kara tashi.
Ana sa ran kungiyar za ta yi taro yau, Litinin, a birnin Vienna, na Switzerland, sannan kuma a gobe Talata, ta yi zaman tattaunawa da Rasha da sauran kashashe.
Daman Kungiyar ta OPEC tare da abokanta da Rasha ke jagoranta suna ta rage yawan man da suke samarwa tun shekara ta 2017, domin ganin farashin man bai fadi ba, yayin da Amurka ke kara yawan wanda take hakowa.
Manyan kasashen kungiyar ta OPEC sun ce sun amince su kara tsawon lokacin rage yawan man da suke fitarwa, amma kuma Iran har yanzu ba ta ce komai ba a game da matakin, a siyasance.
Yawan man da Iran ke fitarwa zuwa kasuwar duniya ya ragu sosai, saboda sabon takunkumin da gwamnatin Amurka ta sanya mata a kan shirinta na nukiliya. Takunkumin da ke kara jefa Iran din cikin matsi.
Dambarwar Amurkar da Iran da raguwar man da Amurkar ke tanada, ya sa farashin ya yi tashi mafi girma a cikin wata guda tun watan Janairu.
Fargabar da ke karuwa wadda dambarwar Amurka da China ta tattalin arziki ta haifar, ta sa farashin man ya yi kasa da sama da kashi 20 cikin dari, kafin harin da aka kai wa jiragen ruwan nan biyu na dakon mai a tekun Fasha, ya yi sanadin kara tashin farashin.
Yayin da Shugaba Trump ke barazanar kara sanya haraji a kan kayayyakin China, abin da ake sa rai shi ne kila ya sake yarda da a samu sasanto kan lamarin.
Masu sharhi dai na sa ran kungiyar kasashe masu arzikin man ta duniya, OPEC ta rage yawan man da kasashen ke fitarwa, har zuwa cikin watan Disamba