Rahotanni na nuna cewa farashin kayan abinci a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.93 cikin 100 a watan Disamba na 2023, daga kashi 32.83 cikin 100 da aka gani a watan Nuwamba 2023.
Ofishin Kididdiga na Kasa, NBS, ya bayyana hakan a cikin ƙididdigar farashin kayan kasuwa, CPI 2023, wanda aka saki ranar Litinin.
Wannan yana wakiltar karuwar kashi 2.72 cikin 100, idan aka kwatanta da adadin da aka gani a watan Nuwamba.
Rahoton ya nuna karuwar kashi 10.18 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin da aka gani a daidai wannan lokacin a cikin 2022.
Hauhawar farashin abinci na wata-wata ya faru ne sakamakon hauhawar farashin mai, nama, burodi da hatsi, dankali, dawa & sauransu.