
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta kara firashin man fetur daga N140.80 zuwa N143.80 a duka kan lita guda.
Hukumar kayade firashin ma fetur (PPPRA) ta sanar da karin kashi 16 cikin 100 na firashin man a wata sanarwa da shugabanta ya fitar a ranar Laraba.
A farkon watan Afrilu 2020, gwamnatin Najeriya ta sanar da ragin firashin man zuwa N123.50 a duk lita guda.
- ‘Man fetur É—in da Najeriya ke sayowa na da guba’
- Fyade a Kano: Mutumin da ‘ya yi wa mata 40 fyade’ ya amsa laifinsa a gaban kotu
Sama da shekaru 20 yanzu firashin mai bai taba zama daidai ba a Najeriya. Wani lokaci ya hau wasu lokutan kuma a samu ragi.
Yadda firashin man yake tsakanin 2000 – 2020
- A Yuni 2000, an siyar da man akan N22 duk lita guda.
- 1 ga watan Janairu 2002, firashin ya karu daga N22 zuwa N26 duk lita.
- 23 ga watan Yuni 2003, gwamnati ta kara firashin daga N26 zuwa N40 lita guda.
- 29 ga watan Mayu 2004, gwamnatin tarayya ta kara firashin daga N40 zuwa N50 duk lita.
- Augustan 2004, firashin ya sake sauyawa daga N50 zuwa N65 a kan lita guda.
- 27 ga watan Mayu 2007, mutane sai sun bada N75 za a siyar musu da fetur a kan lita. Mutane sun yi zanga-zanga, wannan ya sa aka rage firashi zuwa N65 akan lita guda a watan Yuni 2007.
- 1 ga watan Janairu 2012, gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudin zuwa N141 a kan lita. An sake gudanar da zanga-zanga, dubbai sun fito domin nuna adawar karin kudin man, an yi wa zanga-zangar taken #OccupyNigeria. Gwamnati a wannan lokaci sai ta rage firashin zuwa N97.
Hakkin mallakar hoto
Other
- 18 ga watan Janairu 2015 – darajar faduwar firashin a kasuwar duniya, tsohuwar ministan man fetur, Diezani Allison Madueke ta rage firashin daga N97 zuwa N87.
- A Mayun 2016, firashin ya sake karuwa zuwa N145 a kan lita guda, Ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya ce an yi kiran ne domin daidaita firashin da Najeriya ke siyo man daga ‘yan kasuwa saboda karancin man.
- A watan Maris 2020 – faduwar daraja a kasuwar duniya ta sake tilastawa gwamnatin rage kudin man daga N145 zuwa N125.
- Bayan wata guda, a karo na biyu a watan Mayun 2020, hukumar kayyade firashin ta PPPRA ta sanar da sabon firashi daga N121.50 zuwa N123.50 lita guda.
Najeriya na daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da danyen man fetur amma dalilan da gwamnati ke bayarwa na hawa da saukan firashin a galibin lokuta watakila baya raba nasaba da yadda firashin ke sauyawa a kasuwar duniya.
”Bayan nazari kan yadda kasuwar man ya kasance a watan Yuni da kuma duba kudaden da ‘yan kasuwa ke fitarwa wajen sayen man, muna shawarta karin kudin man daga N140.80 zuwa N143.80 a kan kowacce lita daga watan Yuli 2020,” yadda hukumar kayyade firashin mai na kasar PPPRA ta bayyana karin kenan a wata sanarwar da ta fitar ranar 1 ga watan Yuli, 2020.
Sanarwar ta shawarci dukkanin ‘yan kasuwa su sayar da man bisa sharudan PPPRA.