Farashin doya ya yi ƙasa a yayin da sabuwa ta fara isa kasuwanni

Farashin doya ya yi ƙasa a kasuwanni a yayin da sabuwa da aka girbe ke shiga kasuwa kamar yadda jaridar Daily Trust ta tabbatar.

Sabuwar doyar da aka girbe na bawa masu saya zaɓin farashi mai sauki  duk da cewa ragowar tsohuwar da ta rage har yanzu tana da tsada.

Uwargida Theresa Bala wacce take sayar da doya ta faɗawa jaridar Daily Trust a Jos cewa farashi ya sauko sosai na doya sabuwa ta ƙara da cewa ƙwayar doya guda 5 ana sayar da su tsakanin ₦5000 zuwa 8000 ya danganta da girmansu.

Kamar haka na tsohuwar doya ana sayar da su sama da ₦20,000.

Amma kuma ana sayar da ƴan ƙananu a farashi ƙasa da haka daga ₦2000 zuwa ₦3500.

Theresa wacce take saro doya daga Kachia zuwa kasuwar Farar Gada dake Jos a jihar Filato ta ce za a cigaba da kawo doya zuwa jihar  har sai wacce ake nomawa daga yankin Shendam ta fara shigowa kasuwa.

Ta ce yawanci  kuɗin mota shi ne ma’aunin da ake amfani da shi wajen saka farashin.

A kasuwar Akwanga dake jihar Nasarawa ana cigaba da samun sabuwar doyar a cikin kasuwa dake bawa masu zaɓen mai sauƙin farashi.

Da ₦6000 mutum na iya samun doya har guda huɗu ya danganta da girmansu.

More from this stream

Recomended