Farashin kankara a cikin babban birnin Kano ya yi faɗi daga Naira 700 zuwa 150 sakamakon hazo da sanyin yanayi da mazauna garin suka fara fuskanta tun ranar Lahadin da ta gabata.
A makon da ya gabata ne aka siyar da farar ƙankara ta cikin ledar santana a tsakanin Naira 600 zuwa N700 yayin da aka siyar da wani da aka fi sani da “pure water” a kan Naira 200 zuwa 300 sakamakon yawaitar bukatu da aka yi a lokacin Azumin Ramadan saboda zafi.
To sai dai a ranar Juma’a a wasu wurare a cikin birnin an fahimci cewa farashin kayayyakin ya ragu matuka, kuma an sayar da ledar fiyawota a kan Naira 100 zuwa N150 yayin da girman leda Santana ya kai zuwa 200.