Fadar shugaban ƙasa ta hana tallan yaƙin neman sake zaɓen Tinubu a 2027

Fadar shugaban kasa ta bukaci  masu ɗaukar nauyin kayayyakin tallan  sake  neman zaɓen shugaban ƙasa Tinubu a shekarar 2027 da su gaggauta dakatawa.

A wata sanarwa ranar Lahadi, Bayo Onanuga mai magana da yawun shugaban ƙasar ya bayyana cewa yakin neman zaben ya yi wuri kuma ya ci karo da dokar ƙasa.

Onanuga ya ce a sassa daban-daban  na Najeriya ana ƙara samun karuwar allunan tallan takarar shugaban ƙasa Tinubu.

Ya ƙara da cewa suna godewa magoya bayan kan shauki da biyayya da suke wa gwamnatin amma har yanzu dokar zaɓe ta hana gudanar da yakin neman zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

“A matsayinsu na jagorori masu bin doka  shugaba Tinubu da mataimakinsa Shettima basa goyon bayan duk wani abu da zai yi zagon ƙasa ga hukumomi da kuma tsarin gudanar da zaɓe.”

More from this stream

Recomended