Euro 2020: Karim Benzema na cike da murnar ci wa Faransa kwallo

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Karim Benzema ya yi farinciki da ya ci wa tawagar Faransa kwallo a gasar Euro 2020, bayan da suka tashi 2-2 da Portugal ranar Laraba.

Benzema ne ya ci wa Faransa kwallo na biyu a ragar Porugal a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Cristiano Ronaldo ne ya zura kwallo biyu a ragar Faransa a bugun fenariti da hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Ali Deai na Iran mai tarihin yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya mai 109.

Kwallon da Benzema ya ci a bugun fenariti shi ne na 28 da ya ci wa tawagar Faransa, tun bayan kusan shekara shida rabon da ya buga mata tamaula.

A rukuni na shida da suka yi wasan karshe ranar Laraba, Faransa za ta buga Quarter finals da Switzerland ranar Litinin 28 ga watan Yuni da za su kara a Arena Naționala.

Portugal mai rike da kofin za ta kece raini da Belgium, wadda take ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda da za su yi wasan ranar Lahadi 27 ga watan Yuni a Estadio La Cartuja.

Jamus kuwa za ta buga karawar daf da na kusa da na karshe da Ingila a Wembley ranar Talata 29 ga watan Yuni.

More from this stream

Recomended