Emefiele ya lalata tattalin arziki Najeriya—Tinubu

An lalata tsarin hada-hadar kudi na Najeriya a karkashin gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele, wanda aka dakatar, in ji shugaba Bola Tinubu a ranar Juma’a a birnin Paris.

Shugaban na mayar da martani ne kan kama Mista Emefiele da aka yi kwanan nan, inda ya ce tsarin kudin kasar ya “rube” a karkashin tsohon shugaban bankin.

Tun a ranar 10 ga watan Yuni ne Mista Emefiele ke hannun hukumar ‘yan sandan sirri ta SSS, biyo bayan dakatar da shi daga aiki da shugaban kasar ya yi.

Bayan kama shi, ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya ce ana bincikar Mista Emefiele.

More from this stream

Recomended