El-Rufai yana so a dinga yi wa masu fyade dandaƙa

El-Rufai

Hakkin mallakar hoto
KADUNA STATE GOVERNMENT

Image caption

Gwamna El-Rufai ya ce an samu karuwar fyade a jiharsa inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Malam Nasir el-Rufa’i, ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade ita ce yi wa masu aikata laifin dandaƙa.Malam Nasir ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom ranar Asabar.An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Su wane ne mahalarta taron?Baya ga gwamnan jihar Kaduna, akwai ministar harkokin mata da shugabar hukumar NAPTIP da matan gwamnonin jihohin Niger da Kaduna da Kebbi.Sauran mahalartan sun hada da ‘yan jarida da masu fafutuka da wakilan kungiyoyin Kare hakkin bil’adama da kuma lauyoyi. Me sauran masu ruwa da tsaki suka ce?Malam Nasiru ya ce a cire kayan aiki a kuma dinga yanke hukuncin daurin rai da rai kan masu aikata fyade.Ya kara da cewa akwai bukatar iyaye mata su dinga tarbiyyantar da ‘ya’yansu maza wajen ganin girman mutuncin mace da gudun keta haddinta.Ita kuwa ministar mata Pauline Tallen ta fadi abubuwan da gwamnati ke yi na kokarin hada karfi a ciki da wajen kasa don yakar fyade.Matar gwamnan jihar Niger Mrs Lolo kuwa bayani ta yi a likitance kan yadda mace da aka yi wa fyade ke shiga uku ko da bayan ta girma ta yi aure.

Hajiya Zainab Bagudu matar gwamnan Kebbi ma ta yi magana a kan aiyukan da ke kasa.Ita kuwa matar gwamnan Kadunan Ummi el-Rufa’i ta yi kira ne da a fito a yi aiki don kawo karshen wannan matsala.Daga cikin ‘yan jarida da suka yi magana akwai Hajiya Rafat Rafat Salami mai fafutuka kuma ma’aikaciya a gidan rediyo Muryar Najeriya, wacce ta ce akwai bukatar horas da ‘yan jarida don kiyaye fallasa wadanda aka yi wa.Me ya sa aka shirya taron?Wata kungiya mai zaman kanta mai yaki da fyade the movement against rape and sexual violence ya shirya taron.Ta yi hakan ne da nufin wayar wa da mutane kai da ilimantar da su kan yadda za a hada hannu a magance matsalar.Sauran abubuwan da taron ya mayar da hankali akai sun hada da:• Abin da ya da ake bukatar sauya dokokin fyade• Kawo karshen al’adar yin gum da baki• Ji daga bakin likitocin mata kan barzanar da fyade ke yi wa lafiya.• Rawar da kafafen yada labarai za su taka wajen kawo karshen yin gum da baki, da wasu da dama.

Mene ne fyade?

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dakta Nu’uman Habib, masanin halayyar dan Adam ne a Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya ne, kuma a cewarsa, “fyaɗe yana nufin haike wa mata, wani sa’in ma har maza ba tare da izininsu ba, ba tare da sahalewarsu ba, ba tare da yardarsu ba.”

Dakta Nu’uman ya ce tasirin fyaɗe na da girma musamman a rayuwar yara, don kuwa ya kan daɗe a kwakwalwarsu kuma ya jefa su cikin damuwa da tsoro da rashin yarda da amincewa.

“Duk wanda suka haɗu da shi sai su yi tsammanin mai irin wannan halayyar ne. Kuma damuwar takan daɗe tare da su a cikin kwakwalawarsu kusan ta sa ma su sukurkuce”, a cewarsa.

Sai dai bisa alama jama’a ba su gane haka ba, don kuwa ba a cika tattauna batutuwan da suka shafi fyade ba, bare a bai wa wanda a ka yi wa taimakon da ya dace.

Idan aka yi wa wata ko wani fyaɗe, shi da iyalansa sukan zage dantse su tabbatar mutane ba su sani ba. Wannan ba ya rasa nasaba da ƙyama da ake nuna wa waɗanda aka yi wa fyaɗe da iyalansu.

Kuma wannan yana hana jami’an tsaro yin aikinsu yadda ya kamata, musamman ta fannin bincike da yanke hukunci ga wanda ya aikata laifin.

More News

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...

An yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa da majalisar ƙasa kan dawo da Sarki Sanusi

Wasu masu zanga-zanga sun yi jerin gwano ya zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokokin ta tarayya kan dawo da Sarki Muhammadu...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ya kuma sanar da sake naɗa, Muhammad Sanusi a matsayin...

Sanusi ya sake zama Sarkin Kano

Shekaru hudu bayan sauke Muhammadu Sanusi II daga matsayin Sarkin Kano, Gwamna Abba Yusuf, na jihar Kano ya mayar da shi kan karagar mulki.Gwamnan...