
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai a ranar Alhamis ya ziyarci gidan gyaran hali dake jihar Kaduna inda ya duba tsohon shugaban ma’aikatansa, Bashir Sa’idu wanda aka tsare shi a can.
A ranar Litinin ne aka kama tsohon shugaban ma’aikatan gwamnan aka kuma gurfanar da shi a gaban wata kotun majistire dake Rigasa wacce ta tasa keyarsa zuwa gidan gyaran halin kan zargin da ake masa na aikata al-mundahanar kuɗaɗe da sauran tuhume-tuhume.
Wakilin jaridar Daily Trust dake gidan gyaran halin ya ce tsohon gwamnan ya isa gidan tare da rakiyar wasu tsofaffin kwamshinoni da misalin ƙarfe 10:19 ya kuma tafi da 10:47 na safe.
Tsofaffin kwamshinonin da suka raka shi sun haɗa da na ilimi Jafaru Sani, ta ayyukan jin kai da cigaban jama’a, Hafsat Baba da kuma na Muhalli Ibrahim Hussaini.
Bayan kammala ziyarar gwamnan ya ƙi cewa komai bayan da aka nemi jin ta bakinsa.