Tsohon gwamnan jihar Kaduna,Mallam Nasiru El-Rufai ya ziyarci Sanata Abdul Ningi a ranar Juma’a.
Tsohon gwamnan ya ziyarci Sanatan ne a gidansa dake Abuja kawo yanzu ba a bayyana wani dalili ba na maƙasudin ziyarar..
Ziyarar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da majalisar dattawa ta dakatar da Ningi na tsawon watanni uku bayan da yayi zargin cewa an yi cushe a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.
A ƴan kwanakin nan tsohon gwamnan na jihar Kaduna yana yawan kai ziyara ga manyan ƴan siyasa dake ƙasarnan ciki har na jam’iyun adawa.
Ko da a ranar Alhamis tsohon gwamnan ya kai ziyara hedkwatar jam’iyar SDP ta ƙasa.