El-Rufa’i Ya Shawarci Mutanen Zamfara Su Shiga Jam’iyyar ADC Domin Fuskantar Kalubalen Tsaro Da Tattalin Arziki

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya yi kira ga mutanen Jihar Zamfara da su shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) domin hada karfi da karfe wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki a jihar da ma kasa baki daya.

El-Rufa’i ya yi wannan kira ne a yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar ADC a Gusau, babban birnin jihar, a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa jam’iyyar na da tsare-tsaren inganta tsaro, bunkasa tattalin arziki da tabbatar da wadataccen abinci a jihar Zamfara.

Ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da zama masu hadin kai tare da guje wa duk wani abu da zai kawo rabuwar kai a cikinsu. Haka kuma, ya shawarce su da su hada kai da matasa da kungiyoyin mata domin yada manufofin jam’iyyar a matakin tushe.

El-Rufa’i ya kuma tunatar da al’umma muhimmancin shirya katin zabe na dindindin (PVC) tun kafin zabukan 2027, domin su samu damar zaben shugabannin da za su kawo ci gaba mai dorewa.

A nasa jawabin, Mataimakin Sakatare na Tsare-Tsaren Jam’iyyar ADC a matakin kasa, Alhaji Abubakar Atiku, ya bayyana cewa ziyarar El-Rufa’i za ta kara karfafa dangantaka da hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar a jihar.

Shugaban jam’iyyar ADC na Jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Garba, ya ce taron ya samu halartar matasa da mata daga kananan hukumomi 14 na jihar, yana mai jaddada cewa jam’iyyar na kara samun karbuwa da sabbin mambobi a kullum.

Taron ya kuma ja hankalin ‘yan siyasa, malaman addini da sauran manyan masu ruwa da tsaki na al’umma a Zamfara.

More from this stream

Recomended