EFCC ta yi babban kamu bayan ta yi nasarar cafke ƴan damfara

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wasu tagwaye Taiwo da Kehinde Adio tare da wasu mutane biyar bisa zargin zamba ta intanet a Ibadan, jihar Oyo.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, a Abuja.

A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 7 ga watan Disamba a yankin Apete da Apata da ke Ibadan, biyo bayan sa ido da bayanan sirri kan zargin da ake musu na aikata laifukan da suka shafi intanet.“Sauran mutane biyar da ake zargin su ne Jeremiah Gabi, Dennis Gomina, Adepoju Ibukun, Olabode Opeyemi da Adewumi Ayomide.

“Hakazalika rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta mika wasu mutane uku da ake zargi da damfarar yanar gizo ga hukumar EFCC shiyyar Ibadan a ranar 7 ga watan Disamba. ‘Yan sanda sun kama su ne a lokacin da suke sintiri.

“Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa daya daga cikin mutane ukun da ake zargi ba shi da hannu a zamba ta intanet kuma an sake shi nan take ba tare da wani sharadi na beli ba.

“Sauran mutane biyar da ake zargin su ne Jeremiah Gabi, Dennis Gomina, Adepoju Ibukun, Olabode Opeyemi da Adewumi Ayomide.

“Hakazalika rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta mika wasu mutane uku da ake zargi da damfarar yanar gizo ga hukumar EFCC shiyyar Ibadan a ranar 7 ga watan Disamba. ‘Yan sanda sun kama su ne a lokacin da suke sintiri.

“Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa daya daga cikin mutane ukun da ake zargi ba shi da hannu a zamba ta intanet kuma an sake shi nan take ba tare da wani sharadi na beli ba.”

More from this stream

Recomended