EFCC Ta Musanta Zargin Yi wa ‘Yan Adawa Da Shugaba Buhari Bi Ta da Kulli

[ad_1]

Shugaban hukumar hana zarmiya, cin hanci da rashawa ko EFCC a takaice, Ibrahim Magu, ya musanta cewa hukumar ta na yiwa masu adawa da shugaban Nigeria Muhammad Buhari bi ta da kulli.

Ibrahim Magu ya musanta hakan ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar dake birnin Ibadan.

Taron ya samu halartar kungiyoyin farar hula da kungiyoyin addinai da kwararru. Ibrahim Magu ya ci gaba da cewa cin hanci shi ne abu daya da yake mayar da hannu agogo baya ga ci gaban Nigeria, musamman yadda yake shafar talakawa a karkara. A cewarsa saboda haka yaki da cin hanci da rashawa ba yaki ba ne kawai, ceton rayuwa ne. Magu yace, cin hanci ya yiwa kasar illa don haka dole ne a yakeshi.

Hukumar ta EFCC ta kai kararraki kotu fiye da 120 tsakanin watan Fabrairu zuwa watan Agustan wannan shekara.

Shiko shugaban kungiyar Shafa’udeen Islam, Farfesa Sabitu Olagoke, ya ce da tun farko kasar na da hukuma irin EFCC da an dade da ci gaba. Shi ko shugaban kungiyar Kiristocin Nigeria reshen jihar Oyo Pastor Benjamin Akanmu ya ce zasu ci gaba da ilmantar da jama’a akan illar cin hanci da rashawa. Ita ko shugabar hukumar wayar da kawunan jama’a a jihar Oyo Uwargida Dolapo Dosunmu, cewa ta yi “muna iya fara yaki da cin hanci da rashawa tun daga cikin al’umma na kasa har mu kaiga manya na sama”

A saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...