EFCC ta kama wasu daliban Jami’ar Bayero

Hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta ce jami’anta sun kama mutane 25 da ake zarginsu da aikata zamba ta intanet a jihar Kano.

A wata sanarwa ranar Laraba, hukumar ta ce an kama mutanen ne ranar Litinin a unguwar Danbare dake kallon sabuwar Jami’ar Bayero.

A cewar sanarwar an yi kamen ne bayan da aka samu bayanan sirri na aikata damfara ta intanet da mutanen su ke.

“Dukkanin wadanda ake zargin da aka kama an tabbatar da dalibai ne da su ke karatun digiri a jami’ar Bayero,” a cewar sanarwar.

“Wadanda ake zargin sun hada da Ismaíl Nura, Suuleyman Ayeh, Usman Abdulrazaq, Emmanuel Chigozie, Akabe Seth, Daniel Imoter, Abdulganiyu Jimoh da Jafar Abubakar.

“Sauran su ne Usman Nuraddeen, Mohammad Adnan, Abubakar Abusufyan, Abdulmalik Ibrahim, Abubakar Sadiq, Daniel Masamu, Abdulrasheed Abdulsamad, da Issac Dosunu.”

Har ila yau akwai “Nuraddeen Ogunbiyi, Onyeyemi Kaleem, Miracle Joseph, Danjuma Musa, Ibrahim Mubaraq, Yusuf Salihu, Lawal Ibrahim Edebo, Abdulmajeed Suleiman, da Dauda Abdulhamid.”

Hukumar yaki da cin hancin ta ce kayayyakin da aka kama a tare da mutanen sun hada da Laptop, wayoyin hannu, mota kirar Honda da na’ urar rarraba intanet.

Ta kara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

More from this stream

Recomended